Posts

Abdussalam Abubakar ga Tinubu: Ƴan Nijeriya fa na son ganin canji na gaggawa

Image
T sohon shugaban kasa, Abdulsalami Abubakar, ya bukaci gwamnatin tarayya da ta kara himma wajen kawo sauyi a kasar, yana mai cewa ƴan Najeriya na son ganin an samu sauyi cikin gaggawa. Abubakar ya bayyana haka ne a lokacin da ministan yada labarai da wayar da kan jama’a, Mohammed Idris, ya kai masa ziyarar ban girma tare da tsohon shugaban kasa, Janar Ibrahim Babangida a Minna a jiya Lahadi. A cewar wata sanarwa da mataimakin daraktan yada labarai da hulda da jama’a na ma’aikatar yada labarai da wayar da kan jama’a, Suleiman Haruna ya fitar, Abubakar ya taya ministan murnar nadin nasa. Yayin da yake bayyana kwarin gwiwa kan yadda ministan zai iya daga darajar gwamnati a wannan mawuyacin lokaci, Janar din mai ritaya ya ce: “aikin kakaki aiki ne mai wuyar gaske, domin tallata martabar gwamnati a cikin mawuyacin hali. “Gwamnatin ta fuskanci yanayi mai matukar wahala kuma ta gaji kalubale da dama ta fuskar tattalin arziki, tallafin man fetur, da kuma tsaro. “’Yan Najeriya, a matsayinsu na ...

Ma'aikatan lafiya dubu 400 sun yi kadan a Nijeriya, in ji ministan lafiya

Image
Ministan lafiya da walwalar al'umma, Ali Pate, ya ce ma'aikatan kiwon lafiya 400,000 a Najeriya ba su isa ba wajen biyan bukatun kiwon lafiyar ƴan Najeriya. Pate ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ranar Asabar a Abuja, bayan ganawar kwanaki uku da ya yi da sassa da hukumomin da ke karkashin ma’aikatar. Ma'aikatar ta shirya taron ne domin fitar da wani tsari na tsarin kiwon lafiya a Najeriya. A cewar Pate, ma’aikatan fannin lafiya dubu 400,000 sun hada da ma’aikatan kiwon lafiya na al’umma, ma’aikatan jinya, ungozoma, masu hada magunguna, likitoci, masana kimiyya, masu fasaha da kuma mataimaka masu aiki a tsarin kiwon lafiyar Najeriya. "Ba su isa ba idan kuna tunanin cewa wannan adadin zai iya kula da mutane miliyan 220. Tsarin likitanmu ga jama'a ya yi ƙasa da abin da Hukumar Lafiya ta Duniya ke tsammani. “Don haka har yanzu akwai sauran damar samar da ƙari har ma a samu tara saboda a duniya, akwai karancin ma'aikatan kiwon lafiya...

Murja Ibrahim

Image
 Gwamnatin Kano karkashin jagorancin Abba Gida Gida za ta yi wa jarumar TikTok Murja Ibrahim Kunya aure a cikin zawarawan da za su amarce nan gaba.  Shin Mai zakuce ?

Innalillahi wa Inna ilaihi Raji'un

Image
 A llah ya yiwa Sheikh Abubakar Giro Argungu Rasuwa. Marigayin ya rasu ne bayan jinya da yayi na 'dan lokaci a Birnin kebbi.  Za'a masa sallar janaza Gobe  Alhamis 7/9/2023 A Birnin Kebbi. insha Allah. Allah ya gafarta masa Amin.

Tirabunal ta tabbatar da Natasha a matsayin wacce ta lashe zaɓen majalisar dattawa na Kogi ta tsakiya

Image
Kotun sauraren ƙararrakin zaɓe da ke Lokoja, a yau Laraba ta tabbatar da nasarar zaɓen da Natasha Akpoti-Uduaghan ta yi na mazabar Kogi ta Tsakiya a Majalisar Dattawa, ƙarƙashin jam'iyar PDP. Shugaban Tirabunal ɗin, Justice K.A. Orjiakoin, a hukuncin da ya yanke, ya ce Natasha ta samu kuri'a 54,064, inda ta doke abokin takarar ta Sadiku Ohere wanda ya samu kuri'a 51,291. Orjiakoin ya kuma umarci Ohere da ya biya Natasha Naira dubu 500 kuɗin da ta kashe kan ƙarar da aka shigar da ita.

Tirabunal ta tabbatar da nasarar zaɓen Abdulmumin Kofa a matsayin ɗan majalisar dokoki a Kano

Image
 K otun sauraren kararrakin zabe ta Majalisar Wakilai da Majalisar Dokoki a jihar Kano da ke zamanta a Kano ta kori ƙarar da Muhammad Said kiru na APC ya shigar domin kalubalantar nasarar zaɓen majalisar wakilai na mazabar Kiru da Bebeji da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu da Abdulmumin Jibrin Kofa ya lashe. Kotun ta ce Kuru, tsohon Kwamishinan Ilimi, ya gaza wajen gabatar da shedu da dama don tabbatar da cewa ba a yi musu adalci ba a yayin gudanar da zaman Majalisar Wakilai ta Kiru/Bebeji, inda hakan ya karya ƙarar da ya shigar a bisa nasarar  Kofa na jam'iyyar NNPP. Alkalin kotun mai kwamitin mutum uku da ke jagorantar shari’ar, Ngozi Flora ta ce takardun da bangarorin biyu suka gabatar a gaban kotun sun nuna Abdulmumini Jibrin Kofa ya yi murabus daga mukaminsa na babban sakataren hukumar gidaje ta tarayya, kwanaki 30 gabanin gudanar da zaben da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu. 2023 a kan ikirarin mai shigar da kara. Mai shigar da kara ya kasa bada ƙwaƙƙwara...