Tirabunal ta tabbatar da Natasha a matsayin wacce ta lashe zaɓen majalisar dattawa na Kogi ta tsakiya
Kotun sauraren ƙararrakin zaɓe da ke Lokoja, a yau Laraba ta tabbatar da nasarar zaɓen da Natasha Akpoti-Uduaghan ta yi na mazabar Kogi ta Tsakiya a Majalisar Dattawa, ƙarƙashin jam'iyar PDP.
Shugaban Tirabunal ɗin, Justice K.A. Orjiakoin, a hukuncin da ya yanke, ya ce Natasha ta samu kuri'a 54,064, inda ta doke abokin takarar ta Sadiku Ohere wanda ya samu kuri'a 51,291.
Orjiakoin ya kuma umarci Ohere da ya biya Natasha Naira dubu 500 kuɗin da ta kashe kan ƙarar da aka shigar da ita.
Comments