Tirabunal ta tabbatar da nasarar zaɓen Abdulmumin Kofa a matsayin ɗan majalisar dokoki a Kano
K
otun sauraren kararrakin zabe ta Majalisar Wakilai da Majalisar Dokoki a jihar Kano da ke zamanta a Kano ta kori ƙarar da Muhammad Said kiru na APC ya shigar domin kalubalantar nasarar zaɓen majalisar wakilai na mazabar Kiru da Bebeji da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu da Abdulmumin Jibrin Kofa ya lashe.
Kotun ta ce Kuru, tsohon Kwamishinan Ilimi, ya gaza wajen gabatar da shedu da dama don tabbatar da cewa ba a yi musu adalci ba a yayin gudanar da zaman Majalisar Wakilai ta Kiru/Bebeji, inda hakan ya karya ƙarar da ya shigar a bisa nasarar Kofa na jam'iyyar NNPP.
Alkalin kotun mai kwamitin mutum uku da ke jagorantar shari’ar, Ngozi Flora ta ce takardun da bangarorin biyu suka gabatar a gaban kotun sun nuna Abdulmumini Jibrin Kofa ya yi murabus daga mukaminsa na babban sakataren hukumar gidaje ta tarayya, kwanaki 30 gabanin gudanar da zaben da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu. 2023 a kan ikirarin mai shigar da kara.
Mai shigar da kara ya kasa bada ƙwaƙƙwarar hujja cewa an tafka magudi a zaben ba tare da bin dokar zabe ta 2022 kamar yadda aka gyara ba.
"Ana kori wannan mai kara saboda rashin cancanta.
Kotun ta kuma horo mai kara da ya baiwa wanda yake kara Naira dubu 100.
Comments