Ma'aikatan lafiya dubu 400 sun yi kadan a Nijeriya, in ji ministan lafiya
Ministan lafiya da walwalar al'umma, Ali Pate, ya ce ma'aikatan kiwon lafiya 400,000 a Najeriya ba su isa ba wajen biyan bukatun kiwon lafiyar ƴan Najeriya.
Pate ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ranar Asabar a Abuja, bayan ganawar kwanaki uku da ya yi da sassa da hukumomin da ke karkashin ma’aikatar.
Ma'aikatar ta shirya taron ne domin fitar da wani tsari na tsarin kiwon lafiya a Najeriya.
A cewar Pate, ma’aikatan fannin lafiya dubu 400,000 sun hada da ma’aikatan kiwon lafiya na al’umma, ma’aikatan jinya, ungozoma, masu hada magunguna, likitoci, masana kimiyya, masu fasaha da kuma mataimaka masu aiki a tsarin kiwon lafiyar Najeriya.
"Ba su isa ba idan kuna tunanin cewa wannan adadin zai iya kula da mutane miliyan 220. Tsarin likitanmu ga jama'a ya yi ƙasa da abin da Hukumar Lafiya ta Duniya ke tsammani.
“Don haka har yanzu akwai sauran damar samar da ƙari har ma a samu tara saboda a duniya, akwai karancin ma'aikatan kiwon lafiya, akwai kusan karancin mutane miliyan 18," in ji shi.
Comments